Barka da wannan lokaci Zan bada Dan takaitaccen Bayani Game da #NDC da kuma Zaben da yake karatowa. NDC wato Near Digital Collective, Wani bangare ne daga cikin Near Ecosystem wanda yake da alhakin kare haqqin yan kungiya da kuma kula da ma adanai na NEAR domin rabawa zuwa wanda suka cancanta musamman developers da kuma Masu tsara shirye Shirye na cigaban Ecosystem. Akwai Seats guda 29 na shugabancin yan wannan Kungiya ta NDC wanda aka raba su zuwa gida 3 House of merit 15 Council of Advisors 7 Transparency Commission 7 Ko wanna ofis suna da alhakin su da kuma matakai da zasu cika kamin su zama daya daga cikin wanna ofis. House of merit: masu kula da budget Council of advisors: Shawara da kuma dakatar da budget din da bai kamata ba Transparency commission: Hana Cartels suyi participation da kuma korar wanda suka saba kaidojin kungiya Ana bukatar yan takara su mallaki OGSBT kamin yin takara kuma su kasance wanda suka jima a tafiyar NEAR wajen bada tallafi ko ilimi. Wannan shine dan takaitaccen bayani a game da NDC. #BOS @nearhausa.near #NearHausa