Hakika, AI (Artificial Intelligence) fasaha ce da ke sauya yadda muke rayuwa da aiki a duniya. Ta hanyar algorithms da machine learning, AI na iya gano tsari, yin hasashe, da warware matsaloli cikin sauri da inganci fiye da yadda dan Adam zai iya yi a wasu lokutan. Illia Polosukhin, wanda ya taimaka wajen kirkiro transformer model architecture a cikin takardar "Attention Is All You Need", ya yi tasiri sosai a fannin AI. Wannan tsarin ya bada damar samar da AI da ke iya mayar da hankali kan bangarorin data masu muhimmanci, wanda ya inganta yadda AI ke fahimta da kuma aiki da yare daban-daban. Bayan barinsa Google, Illia ya kafa NEARProtocol, wanda ke amfani da fasahar Blockchain don magance wasu kalubalen da AI ke fuskanta, musamman wajen tsaro da sirrin bayanai. NEARProtocol ta yi amfani da Blockchain Operating System (BOS) don samar da wani yanayi inda AI za ta iya aiki cikin 'yanci da kuma inganci. Hakan ya hada da kokarin hadewa da web3, wanda ke nufin sabon yanayi na intanet da ke mai da hankali kan decentralization da user empowerment. NEARProtocol ta ci gaba da zama jagora a fannin hada AI da Blockchain, tana samar da wani ecosystem da ke tallafawa masu kirkiro da masu amfani da fasahar Blockchain da AI a fadin duniya. Wannan hadin gwiwa na AI da Blockchain na da babban tasiri wajen tabbatar da cewa fasahar AI ta zama mai amfani da kuma aminci ga kowa da kowa. @nearhausa