Qoqarin Near na Tabbatar da Chain Abstraction!!! A lokacinda ake ganin akalar Duniya ya maida hankali kan hadin gwiwa dan kawo cigaba a Duniyar Crypto a taron da akayi a ETH-Denver a wasu kwanuka dasuka gabata, a daidai lokacin NEAR ta zo da gaba daya ecosystem dinta zuwa wannan taro dan kyakkyawar baje haja ta musamman, inda megirma Altan Tutar na NEAR FOUNDATION ya bude taron da bayanin sa mai taken “future of DeFi: NEAR protocols role and potential”. Altan yayi bayani a kan shirin NEAR a kan DeFi wanda yake bada muhimmanci a kan fragmentation da modularity. Near tana da niyyar zama platform me hada mutane da manhajojin DeFi a kan blockchain kala kala. Gudumawar NEAR bai takaita anan ba, inda shima makerin nan Illia Polosukhin, CEO kuma Co-founder na NEAR Protocol, ya kara fashin baki a panel din da aka yi na Decentralized AGI summit, inda yayi bayani a kan canjin da yake faruwa a AGI. Bai tsaya nan ba, yayi bayani a kan kirkirar AGI mai zaman kan sa da kuma abubuwan da hakan zai kawo a duniyar decentralization. Illia ya kara da bayani a kan kara habbaka fasahohin AI domin jin dadin community. Hakazalika yayin yacigaba da jawabinsa, Illia ya kara da yin hira da Erik Voorhees a kan decentralization na AI. Sannan ya kara da bayani a kan digital self-sovereignty a zamanin AI kafin mai takarar shugaban kasar Amurka wato Robert F. Kennedy Jr ya hau kan mimbari domin kulle session din da jawabin sa.