Wai shin menen MONOLITHIC kuma ta yaya NEAR protocol suke amfani dashi? Tun farko, NEAR protocol ta kasance L1 blockchain inda ‘data availability’ da kuma tabbatawa da ingancin transactions yake faruwa a cikin ecosystem. Wannan tsari ya bawa NEAR damar bawa mutane da yawa amfani da shi a lokaci guda ta hanyar amfani da fasaha kamar sharding da sauransu. Ita kalmar ‘monolithic’ tana nufin abu wanda aka yi shi a waje daya ba tare da amfani da wani abu daban ba.