1. WITHDRAWAL FUNCTION Mene ne withdrawal function. Farko abun dubawa yanda mai karatu zaifi saurin ganewa shine mu fara sanar dashi menene WITHDRAW tukunna, saboda zaifi ganewa cikin sauki menene withdrawal function ke nufi. WITHDRAW Withdraw hanyace ta cire kudi ko wani abu mallakinka daga wani accounts ko wallets xuwa wani accounts din kamar yadda muka saba a al'amuran mu na yau da kullum MISALI xakaje banki ko wajan mai POS kace kazo withdraw sai ka cire kudinka daga cikin account dinka to hakama yake faruwa da tokens/coins a exchangers. To yanzu mun fahimci mene withdraw. WITHDRAW FUNCTION Withdraw function wani bangarene dake bada dama wajan withdrawing tokens/coins daga exchangers wanda shi wannan bangaren ko muce aiki wanda yawancin exchangers ke anfani dashi wajan bada security ga mamallakin shi wannan accounts din MISALI: Idan ka canza password na CEX dinka yawanci sukan dakatar da withdraw function dinka yadda ko zakayi withdraw bazaiyuba na wasu awanni domin tabbatar da baka tsaro har sai sun turamaka sako ta email dinka na cewa kaine ka canza password idan ka tabbatar da hakan sannan su bude maka withdraw function dinka. Ha ila yau idan kayi kure wajan tura wani tokens kan chain din da banashi yawanci idan harda withdraw function a wancan to tokens dinka zai iya dawowa amma idan babu lokacin rubuta smart contract din to shikenan badama ya dawo sabida babu withdrawal function tattare dashi. 2. NIGHTSHADE Nightshade yana anfani da wata fasaha wadda muke kira ERASURE CODING ALGORITHM, it wannan fasaha ta Erasure tana saukakawa wajan kammaluwar aiki a kankanin lokaci da zarar kaso mafi tsoka daga cikin aikin ya kammala, MISALI da zarar kaso 70% na wannan aikin ya kammala to zai turo aikin gaba daya saboda ba lalle sai kaso 30% din sunzo ba saboda ya riga da yasan meke kunshe dasu, zamanin baya anan anfani da SALOMON-READ wanda shima irin aikin dake aikatawa amma kuma sai yazo da rashin security sai Erasure coding yazo ya maye gurbinsa. Misalin erasure a muamalar mu shine kaine aka baka wannan abun a rubuce akace me ake nufi. "MUSA YA ....... MAKARANTA DA....." To kana karantawa kasan me ake nufi saboda kalmomin da babu ka riga da kasansu kawai zakace "MUSA YA TAFI MAKARANTA DA SAFE" tunda kowa yasan mafi akasari da SAFE ake tafiya makaranta. Wannan shine takaitaccen bayani akan ita wannan fasaha ta ERASURE CODIN. Idan muka dauki misalin dake cikin wannan hoton zamuga cewa datace guda daya amma ta rarrabu zuwa kaso 5 cikin drive kamar yadda shards ke rarrabawa domin saurin wanzar da aikin. To idan kuma muka kalli dayan gefan zamuga a wancan gefen data daya dake cikin drive guda daya tayi failing amma hakan bai hana wanzuwar aikin ba tunda kaso mafi tsoka ya kammal. #Nearhausa @Nearhausa.near