Ko kunsa Jami'ar (University) da ake koyar wa kyauta ba tare da kabiya sisin kobo ba? Wanna jami'ar tana da kwararrun malamai, sanna gashi mafi yawan abun da suke karantarwa Practically ne suke yin sa. Bugu da kari duk wani ilimin ana koyarwa a cikin wanga Jami'ar. Bawai iya karatun boko ne kawai harda na addini sannan harda sana'o'in, duk suna karantarwa kuma kyauta. Sannan ba'a biyar wani registration fee, school fee, accomodations fee da sauran su. Just abun da suke bukata a wurin dalibi be wuce Focus, Data & Time ba. Sunan wannan jami'ar (University) shine International Institute of YouTube (YOUTUBE). Nasan zakuyi mamaki da kukaji sunar jami'ar (University) wai, YouTube. YouTube itace jami'ar da tafi duk jami'o'i duniya yawan malamai da daliban. YouTube an kirkiro tane a ranar 14/02/2005. Aikinta shine ɗura Video, kuma ba'a kayyade wani irin video koh Yaren da za'ayi Amfani da shi kafin a ɗura Video ba. YouTube tana da Active Channels 114Million, wadanda aƙalla suna ɗura Video 1 duk bayan kwana 30, cikin su akwai 2million channel kuma, waɗanda suke samu kudin da channels in mafi akasari waɗannan channels in sune malamai, domin zaka samu suna karantar da illimunka ne daban-daban. YouTube suna da dalibi koh ince Subscribe 2billion wanda akalla sunyi subscribing na channel daya. Duk ilimin da kake son koyo koh koyarwa zaka iya garzayawa YouTube zaka samu karin ilimi akan abinda kake son koyo. YouTube yana tabbatar da maganar masu iya zance da suka ce "Duk Nisan Gari Akwai, Gari A Gabashin" suka kara da cewa "Duk Sammakon Ka Wani A Hanyar Ya Kwana" Duk ilimin da kake son koyo, to ka ziyarar ce YouTube zaka samu wani yariga da yayi bayani akai. Majority daliban ilimi, sun san da haka, kawai dai bama dauka shi da muhimmanci ne, da zarar mun dansamu dakan daga cikin matsalar mu shike bara mu kara komawa ba. A kwai Channels in da muddin ka jure wari bibiyar program nasu InshaAllahu abun da kake son koyo zaka iya shi sosai. Kawai what we need is FOCUS, DATA AND TIME. Allah yayi mana jagora #Near #NearHausa Sanusi Abdulmanaf 05/08/2023